Kannywood

Abinda yasa Adam zango yasaki matarsa kenan

Abinda yasa Adam zango yasaki matarsa kenan

‎Rahotanni daga Arewa Updates sun tabbatar da cewa fitaccen jarumin Kannywood, Adamu A. Zango, ya rabu da matarsa, Maimuna Pretty, bayan saɓanin da ya shiga tsakaninsu a safiyar juma’ar data gabata.
‎
‎Majiyoyi sun ce an yi ƙoƙarin sasanta ma’auratan amma hakan yaci tura. Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Adam A. Zango ko Maimuna Pretty da ta tabbatar ko ta musanta rahotannin rabuwar auren.
‎
‎
‎Wannan shine karo na bakwai da Adam Zango yake sakin matan daya aura tun daga Amina Uba (Maman Haidar) wacce ita ce matar na farko da fara aura, shekaru 19 da suka gabata.
‎
‎Shin ko menene ra’ayinku dangane da yawan rabuwa da Adam Zango yake yi da matayen da ya aura?

Allah yasamudace 🤲

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button